Yadda dawowar Buhari daga Saudiyya ta kasance

12

A ranar Talata da yamma Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan gudanar da ibadar Umara a Saudiyya.

Ranar Alhamis da ta gabata ne Shugaban ya bar Najeriya zuwa Saudiyya don yin Umara.

Jirgin Shugaban Ƙasar ya sauka a Sashin Saukar Jirgin Shugaban Ƙasa na Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin ƙarfe 6:30 na yamma.

Shugaban dai ya je Saudiyya don yin Umara ne bisa gayyatar da Sarkin Saudiyya, kuma Mai Kula da Masallatai Biyu Masu Tsarki, Salman Bin Abdul’aziz ya yi masa.

Shugaban ya samu rakiyar makusantansa zuwa Saudiyyar don yin Umarar.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan