Ko kun san umarnin da Buhari ya ba ministocinsa kafin Ranar Rantsuwa?

182

Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci ministocinsa da su miƙa muƙamansu ranar 28 ga watan Mayu, kwana ɗaya kafin rantsar da shi a wa’adin mulkinsa na biyu.

Shugaban ya bada umarnin ne ranar Laraba yayin gudanar da Taron Tattaunawa na Ban-kwana na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, FEC a Fadar Shugaban Ƙasa dake Villa, Abuja.

Ya lura da cewa Taron Tattaunawar na Ban-kwana shi ne na ƙarshe a wannan Majalisar Zartarwa mai barin gado, kafin rantsar da shi a wa’adin mulkinsa na biyu ranar 29 ga watan Mayu, yana mai ƙarawa da cewa ministocin za su iya ci gaba da aiki har ranar Talata, 28 ga watan Mayu.

Shugaba Buhari ya yaba wa ministocin bisa yadda suka yi wa ƙasar nan hidima a shekaru uku da rabi da suka gabata.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan