Takarar Shugaban Majalisar Dattijai: Sabon Gwamnan Yobe ya bayyana ɗan takarar da yake goyon baya

133

MaiMala Buni, sabon Gwamnan Yobe ya roƙi sanatoci na jam’iyyar APC da su mara wa takarar Sanata Ahmad Lawan a matsayin Shugaban Majalisar Dattijai baya.

Sabon Gwamnan ya yi kiran ne ranar Litinin a wata tattaunawa ta waya da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a Damaturu.

Mista Buni ya ce Lawan, wanda ya zama sanata tun a shekarar 2007 inda yake wakiltar Mazaɓar Sanata ta Yobe ta Arewa ya nuna ƙwarewa, biyayya, jajircewa da rashin son kai da ya kamata shugaba na gari ya nuna.

“Babu shakka Sanata Lawan zai iya bada shugabanci mai inganci wanda ake buƙata don cika alƙawuran yaƙin neman zaɓe da jam’iyyar APC ta yi wa ‘yan Najeriya”, in ji Mista Buni.

Sabon Gwamnan ya ce jam’iyyar APC ta yanke shawarar mara wa takarar Sanata Lawan baya ne don tabbatar da cewa an samu fahimta tsakanin sanatoci da ɓangaren zartarwa, a samu ci gaba cikin gaggawa don inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

“Hikimar da tasa jam’iyyar take mara wa Lawan baya shi ne a tabbatar da cewa ba a yi kuskuren ƙara samun wani shugabanci da zai riƙa ƙalubalantar ɓangaren zartarwa ba a Majalisar Dattijai ta 9, don ci gaban ‘yan Najeriya da dimukoraɗiyya.

“Ba za ki iya cewa ke ce jam’iyya mai mulki ba, amma kina da Majalisa da take kanta a rarrabe, kamar yadda aka gani a shekaru huɗu na ƙalubalantar juna da cin dunduniya.

“Wani yanayi da aka riƙa samun jinkiri na ba gaira ba dalili wajen amincewa da ƙudurori, har da kasafin kuɗi don fusata gwamnati, ba za a ƙyale haka ya sake faruwa ba”, in ji shi.

Ya yaba wa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar bisa mara wa Sanata Lawan baya.

“Ina da kyakkyawan fata cewa waɗanda ke takarar Ofishin Shugaban Majalisar Dattijai daga ƙarshe za su amince da hukuncin jami’yyar, su kuma goya wa ɗan takarar da jam’iyyar ta tsayar baya”, a kalaman Mista Buni.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan