Ƙungiyar Gwamnonin PDP ta zaɓi sabon shugaba

9

An zaɓi Gwamna Seriake Dickson na Jihar Bayelsa a matsayin Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP.

Gwamna Ibrahim Dankwambo na Jihar Gombe, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar mai barin gado ya sanar da haka a ƙarshen taron tattaunawa na Ƙungiyar ranar Laraba a Abuja.

Lokacin da Gwamna Dankwambo yake karanta jawabin bayan taron, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya kafa dokar ta-ɓaci a kan lamarin tsaro.

“Ƙungiyar Gwamnonin PDP ta damu sosai da rashin tsaro da yadda ya shafi tsaron samar da abinci, saboda manoma suna jin tsoron zuwa gonakinsu, saboda tsoron kar a kashe su ko a yi garkuwa da su, tana kira ga Shugaban Ƙasa da ya kafa dokar ta-ɓaci a kan harkokin tsaro”, in ji Gwamna Dankwambo.

Wasu daga cikin gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da Ifeanyi Okowa na Delta, Emmanuel Udom na Akwa Ibom, Samuel Otorm na Benue, Aminu Tambwal na Sokoto, Seriake Dickson na Bayelsa da Emeka Ihedioha na Imo,

Haka kuma akwai Shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki; Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara; Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Uche Secondus; da ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP, Peter Obi.
Bayan kammala zaɓen, sai gwamnonin suka halarci taron Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, NGF, inda suka haɗu da takwarorinsu na jam’iyyar APC, inda aka zaɓi Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin ta Najeriya, NGF.

Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi shi ya yi nasarar zama Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin ta Najeriya, NGF.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan