Jawabin Mai Shari’a Bulkachuwa bayan ta yi murabus

237

Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara, Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa, waddda ta ajiye muƙaminta a matsayin Shugabar Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Shugaban ranar Laraba ta ce ta ajiye muƙamin ne bisa dalilai na ƙashin kai.

Har lokacin da ta ajiye muƙamin ranar Laraba, Misis Bulkachuwa tana jagorantar wani gungun alƙalai biyar, waɗanda za su saurari ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya shigar, inda yake ƙalubalantar nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 23 ga watan Fabrairu, 2019.

Lauya mai kare Atiku, Livy Ozuokwu ya roƙi Misis Bulkachuwa, Shugabar Kotun da ta tseratar da kanta bisa dalilin cewa za ta iya yin son kai a ƙarar.

Lokacin da take sanar da yin murabus ɗinta, Misis Bulkachuwa ta ce: “Ina barin gungun alƙalan ne bisa dalilai na ƙashin kai. Ina farin cikin cewa an warware matsalar “a kan hujjoji da doka”, saboda haka “ba wata alƙaliya da za ta fuskanci irin abinda na fuskanta”.

Koda yake gungun alƙalai biyar na kotun, a wani hukunci da gaba ɗayansu suka amince da shi sun yi watsi da buƙatar yin murabus ɗin, amma Misis Bulkachuwa ta ce ta janye ne bisa dalilai na ƙashin kai.

Mai Shari’a Olabisi Ige, wanda ya karanta matsayin alƙalan, ya ce dangantakar dake tsakanin Mai Shari’a Bulkachuwa da mijinta, Adamu Bulkachuwa, wanda sabon sanata ne, da ɗanta, Aliyu Abubakar, waɗanda dukkaninsu aka zaɓe su a ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC ba ta isa a ce za ta yi son kai a yadda za ta gudanar da shari’ar ba.

Mai Shari’a Ige ya kuma yanke hukuncin cewa ba wata alamar son kai da za a iya gani a jawabin da Mai Shari’a Bulkachuwa ta yi yayin ƙaddamar da zaman Kotun ranar 8 ga watan Mayu, ballai a ce ta riga ta yanke hukunci a kan ƙarar da masu ƙarar suka shigar.

Dukkan alƙalan, har da Mai Shari’a Bulkachuwa sun amince da hukuncin Kotun.

Ta ce za a naɗa wani sabon alƙali da zai jagoranci gungun alƙalan, amma sauran alƙalan huɗu za su ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa lokacin da za a naɗa sabon alƙali.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan