‘Yan bindiga daɗi sun kai sabbin hare-hare a Maberaya

174

Daga Abdurrahman Abubakar Sada

A Lahadin nan, ‘yan bindiga sun afka wa mutanen garin Maberaya, sai dai ba su samu nasara ba.

Haka zalika, ranar Talata sun ƙara dawowa, sun shiga garin Maberaya da safe, sun shiga da yamma. Sai dai a harin ranar Talatar ne suka samu nasarar kashe mutum uku, suka raunata biyu.

Dukkkanin waɗannan munanan hare-hare, an kai su ne a garin Maberaya da ke ƙaramar hukumar Shinkafi, a cikin jihar Zamfara.

Wallahi kullum haka muke kwana haka muke tashi, babu nutsuwa, babu kwanciyar hankali.

Amma duk da haka saboda tsabar wauta, wasu ke yaɗa cewa an samu zaman lafiya.
Allah Ya isa!

Allah Ya kawo mana ƙarshen wannan ibtila’i, Ya kawar mana da wakilai marasa kishin al’umma.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan