APC ta taya Bagudu murna

163

Kwamitin Zartarwa na Ƙasa na Jam’iyyar APC ya taya Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu murna bisa zaɓen sa a matsayin Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, PGF.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Malam Lanre Issa Onilu, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na Jam’iyyar APC ya fitar ranar Juma’a da daddare.

Sanarwar ta ce zaɓen Mista Bagudu abu ne da ya dace.

“Mun lura da nasarorin da Bagudu ya samu a aikin gona, musamman samar da shinkafa a Jihar Kebbi wadda ta yi daidai da manufar faɗada tattalin arziƙi ta gwamnatin APC da Shugaba Muhammadu Buhari ke jawabi.

“Kamar yadda manufofin Ƙungiyar Gwamnonin APC take na samar da shugabanci na gari, tabbatar da ci gaba a dukkan jihohin da APC ke mulki, da kuma bunƙasa shirye-shirye inganta zamantakewar jama’a na jam’iyyar APC, muna da ƙarfin guiwar cewa a ƙarƙashin shugabancin Bagudu, PGF za ta ci gaba da bada gudunmawa wajen ci gaban jam’iyyarmu mai girma, bunƙasa shirye-shiryenmu na ci gaba da ci gaba goya wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari don cika wa ‘yan Najeriya alƙawuran da ta yi musu.

“Muna yi wa Bagudu fatan wa’adin mulki mai nasara a matsayin Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, PGF, in ji sanarwar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan