Kotu ta hana a ba Okorocha Takardar Shaidar Cin Zaɓe

231

Wata Babbar Kotun Owerri ta fitar da wani umarni da ya hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC janye matakinta na ƙin ba Rochas Okorocha Takardar Shaidar Cin Zaɓe.

Ƙarar mai lamba HOW/596/2019, ɗan takarar Sanata na jam’iyyar PDP a Mazaɓar Sanata ta Imo ta Yamma, Onorabul Jones Onyeriri ne ya shigar, inda yake ƙarar INEC.

INEC ɗin tana shirin ba Mista Okorocha Takardar Shaidar Cin Zaɓe ne, abinda yasa Mista Onyeriri ya maka ta a Kotu.

Alƙalin Kotun, Mai Shari’a E.F Njemanze ya umarci da a dawo yadda ake a baya har sai ta kammala jin ƙarar.

An ɗaga ƙarar zuwa 5 ga watan Yuni don ci gaba da sauraro.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan