Gidauniyar Dangote, DF ta tallafa wa mabuƙata Musulmi a jihar Enugu a wani shirinta na Ciyarwa na Watan Ramadan na 2019.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya ruwaito cewa an kayan tallafin ne ga mabuƙata da ba su gaza 500 a Abakaliki ranar Litinin.
Kayan tallafin sun haɗa da katan ɗin pasta 250, buhun gishiri mai nauyin kilogiram 1 guda 500, buhun sikari mai nauyin kilogiram 1 guda 500, buhun Samolina mai nauyin kilogiram 5 guda 500, da buhun alkama ma nauyin kilogiram 10 guda 250.
Ndagi Ahmed shi ne jami’in da ya duba yadda aka raba kayayyakin.
Turawa Abokai