Hakkinmu Ne Mu Ilimantar Da Ƴaƴanmu Domin Zama Masu Daraja Idan Sun Girma –Kwankwaso

98

Tsohon gwamnan jihar Kano, Engr Dr Rabi’u Musa Kwankwaso yayi kira ga iyaye da su cigaba da kulawa da ‘yayansu domin sauke nauyin da yake kansu.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a sakon nuna murnar ga ranar da majalissar dinkin duniya ta ware wa yara duniya, “Ranar Yara” “Children’s Day”.

Sakon daya wallafa a shafinsa na twitter, Kwankwaso yace hakki ne akan wuyan iyaye dama al’umma wajen kula da tsare tarbiyya da Ilimin yara.

“Ya rataya a wuyan mu, mu hadu wajen kulawa, Ilimantar da ‘yayanmu domin su tashi cikin bin dokokinmu da al’adu a matsayinsu na manya masu daraja.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan