Babban Sifeton ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu ya bada umarnin a tura Ahmed Iliyasu a matsayin sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano.
Mista Iliyasu ya karɓi aiki ne daga Wakili Muhammad, wanda aka fi sani da Singham a jihar Kano, wanda ya yi ritaya daga aikin ɗan sanda ranar 26 ga watan Mayu, bayan shafe shekara 35 yana aikin.
Mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa, DCP Frank Mba ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Litinin a Abuja.
Mista Iliyasu, wanda yake da Digiri na Biyu a Nazarin Kasuwanci daga Jami’ar Ambrose Ali dake Ekpoma, har lokacin da aka ba shi wannan muƙami na baya-bayan nan, shi ne Force Provost Marshall a Hedkwatar Rundunar ‘Yan Sanda dake Abuja.
Mista Mba ya ce sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan ya taɓa taɓa zama Kwamishinan ‘Yan Sanda a Jihar Ogun daga shekarar 2016 zuwa Janairu, 2019.
Mai magana da yawun Rundunar ya ce ana sa ran ya yi aiki da gogewar da yake da ita a aikin ɗan sanda da kiyaye doka wajen tafiyar da harkar tsaro mai cike da rikici a Jihar Kano.
Ya ce lokacin da Babban Sifeton ‘Yan Sandan ke taya Mista Wakili murnar gama aiki, ya yi kira ga Mista Iliyasu da ya tashi tsaye don samar da aikin ɗan sanda mai inganci a jihar.
Mista Mba ya ce muƙamin ya fara aiki ne nan take.