Kotu ta hana Gwamnatin Kano kama Mannir Sanusi

175

Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta dakatar da Hukuncin Kotun Majistare wadda ta bada umarnin a kama Mannir Sanusi, Shugaban Ma’aikatan Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II da wasu mutum biyu.

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano ce ta maka Shugaban Ma’aikatan, wanda ke riƙe da sarautar Ɗamburan Kano, tare da Akanta na Masarautar Kano, Sani Muhammad Kwaru sakamakon zargin su da ƙin amsa gayyatarta bisa wata badaƙalar Naira Biliyan 4 da ake zargin Sarki Sanusi da hannu a ciki.

A hukuncin da ya yanke ranar Talata, Babban Magistare Mohammed Idris ya bada umarnin kama mutanen uku bisa zargin ƙin amsa gayyatartar Hukumar da suka yi.

Amma, ranar Talatar da yamma sai ga wani sabon hukunci daga Mai Shari’a S.B Namallam na Babbar Kotun Jiha, wanda ya umarci dukkan masu ƙarar su tsaya a yadda a ke a baya har sai ta gama sauraron ƙarar.

Daga nan sai Kotun ta sa ranar 13 ga watan Yuni don ci gaba da sauraron ƙarar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan