Muhimman Batutuwa 10 Da Buhari ya Furta A Jiya

173

1. Na samu nasara a yaki da Boko Haram. Kafin na hau mulki, sune keda iko da kananan hukumomi 17 a jihar Borno.

2.Tun kafin a gudanar da zabe na san nine zan yi nasara

3. Zan tabbatar da cewar rundunar ‘yan sanda da bangaren shari’a sun cigaba da daukan tsaurararan matakai a kan ‘yan ta’adda

4. Na yi bankwana da majalisar zartar wa da na kafa. Ban tattauna da kowa ba dangane kunshin sabbin ministocin da zan nada.

5. Mun kwato dukiya mai yawa daga hannun wadanda ake tuhuma da laifukan cin hanci. Akwai bukatar taka tsan-tsan a kan harkar yaki da rasha wa, ba abin sauri bane.

6. A kan nadin shugabannin hukumomin tsaro, shugaba Buhari ya ce; “na yi dogaro da bayanan su na aiki ne kafin na nada su.”

7. A kan alakar sa da majalisa, shugaba Buhari ya bayyana cewar; “dole a samu matsala duk lokacin da bangaren majalisa suka fara jin daidai suke da bangaren zartar wa. Na taba taba tambayar Bukola a kan menene ribar sa a cin dunduniyar gwamnati. Na dade da saka shi cikin marasa kishin kasa.”

8. Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya su tona asirin duk wasu masu laifi da marasa gaskiya dake kusa da su

9. “Masu kira na da ‘Baba go slow’ zasu sha mamaki a wannan karon” a cewar Buhari

10. Majalisa bata da wani uzuri na rike kasafin kudi har tsawon watanni bakwai

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan