Saraki, ‘yan Majalisun Tarayya suna shirya wa Magu kutungwila

200

Shugaban Majalisar Dattijai, Dakta Abubakar Bukola Saraki da sauran ‘yan Majalisun Tarayya suna cikin wani faɗa na ƙarshe da Shugaban Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, Ibrahim Magu.

Majalisar Dattijai ta 8, wadda wa’adin shugabancita zai ƙare a farkon watan Yuni da zarar an ƙaddamar da Majalisar Dattijai ta 9, ta kammala shiri tsaf don kawar da shugaban na EFCC, ko kuma su mayar da shi yadda ba za a iya gabatar da sunansa ba ga Majalisar Dokoki mai jiran gado.

Wannan na zuwa ne duk da Sanata Shehu Sani ya soki wannan yunƙuri na gyara Dokar da ta Kafa EFCC.

A cewar Sanata Sani, gyara Dokar EFCC, indai da niyyar ɗaga “matsayin cancancta” ne, to ba a da buƙatar ta.

Shirin da Saraki ke yi na cire Magu na zuwa ne ta hanyar gyara Dokar EFCC (Dokar da ta Kafa ta) ta 2004.

Tun shekarar 2018 aka fara samun takun saƙa tsakanin Shugaban Majalisar Dattijai da Magu lokacin da Saraki ya so ya yi amfani da ƙarfinsa wajen cire shi.

Faɗan ya ci gaba lokacin da aka miƙa sunan Magu a matsayin shugaban EFCC, kuma Majalisar Dattijai ta yi watsi da sunan sakamakon wani rahoto da ta ce ta samu daga Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS.

To, amma ‘yan Majalisun suna neman gyara Dokar kwana 13 kafin wa’adin shugabanci na Majalisar Dokokin ta Ƙasa ta 8 ya ƙare.

Dokar da ake so a gyara tana so ta ba Shugaban Ƙasa ikon naɗa Shugaban EFCC daga jami’in ɗan sanda wanda bai yi ƙasa da Mataimakin Babban Sifeton ‘Yan Sanda ba ko daidai da shi a sauran hukumomin tsaro.

Idan gyaran dokar ya samu amincewa, zai sa Magu ya zama bai cancanta ba, kuma ba za a iya sake gabatar da shi ga Majalisar Dokoki ta 9 ba don amincewa.

Magu Kwamishinan ‘Yan Sanda ne.

A yau Talata ne ake sa ran za a gabatar da dokar a zauren Majalisar Dattijai.

Wani ɓangaren ƙudirin zai mayar da shi wajibi ga EFCC ta samu umarnin kotu kafin ta ƙwace kadarorin waɗanda take zargi.

Saɗarar samun umarnin kotun zai hana EFCC ikon amfani da Saɗarar Ƙwace Kadara ta Wucin Gadi da take amfani da shi ba tare da danganawa da kotu ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan