Abubuwan da zan mayar da hankali a kai- Sabon Gwamnan Borno

206

A ranar Laraba ne aka rantsar da Farfesa Babagana Zulum a matsayin sabon Gwamnan Jihar Borno.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN, ya ruwaito cewa Gwamna Zulum ya yi rantsuwar ne tare da mataimakinsa, Alhaji Umar Kadafur.

Mai Shari’a Kashim Shettima ya jagoranci Bikin Rantsuwar wanda dubban mazauna Maiduguri, shugabannin al’umma da manyan jami’an gwamnati suka halarta.

Gwamna mai barin gado, Kashim Shettima ya ce yana farin cikin miƙa mulki ga mutumin da ya yi fice, kuma ya cancanta, wanda yake da abubuwan da ake buƙata don ciyar da jihar gaba.

Mista Shettima ya yi kira ga al’ummar jihar da su ba sabuwar gwamnatin goyon baya don ba ta damar yi wa al’umma hidima yadda ya kamata.

Ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari, al’ummar jihar, shugabannin al’umma da na addini bisa yadda suka ba shi goyon baya lokacin shugabancinsa.

A jawabinsa na farko, Gwamna Zulum ya yi alƙawarin aiwatar da ajanda 10 don kawo ci gaban tattalin arziƙi da na zamantakewa cikin gaggawa a jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan