Bikin Rantsuwa: Yakubu Gowon ya fitar da Buhari kunya

198

A ranar Laraba ne aka rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari don fara wa’adin mulkinsa na biyu.

To sai dai ba a ga tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan a wajen Bikin Rantsuwar ba.

Haka kuma, ba a ga tsohon Shugaban Mulkin Soja, Ibrahim Babangida ba.

Shugaban Mulkin Soja kaɗai da aka gani a wajen Bikin Rantsar da Buhari da Osinbajo shi ne Janar Yakubu Gowon mai ritaya, wanda ya zauna a kujerar tsakiya daga cikin kujerun da aka tanadar wa mutanen dake wannan aji.

Mista Gowon dai ya kasance mai goyon bayan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, yakan shirya addu’o’i lokaci-lokaci a manyan majami’u a madadin ƙasar nan ƙarƙashin ƙungiyarsa ta Nigeria Pray Movement tare da goyon bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Ɗaya daga cikin irin waɗannan tarukan addu’o’i shi ne wanda Deeper Life Bible Church ta ɗauki nauyi, inda Janar Sufurtandan Majami’ar, Pastor W.F Kumuyi ya jagoranci addu’o’in.

An gudanar da Bikin Rantsar da Buhari ne a Filin Taro na Eagle Square dake Abuja.

Dama Fadar Shugaban Ƙasa ta ce za a yi Bikin Rantsuwar ne saisa-saisa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan