Wa’adin mulki na biyu: Buhari zai yi tafiya ta farko zuwa ƙasar waje gobe

32

A gobe ne Shugaba Muhammadu Buhari zai yi tafiya zuwa Saudiyya domin wata ziyarar aiki, in ji jaridar Daily Trust.

Shugaban zai yi tafiyar ne sa’o’i kaɗan bayan rantsar da shi a wa’adin mulki na biyu.

Idan dai ba a manta ba, Shugaban ya je Saudiyya daga 16 zuwa 21 ga watan Mayu inda ya gudanar da Umara.

Wasu majiyoyi a Fadar Shugaban Ƙasa sun shaida wa Daily Trust cewa an kammala dukkan shirye-shiryen wannan tafiya ta Shugaban Ƙasa.

Ɗaya daga cikin majiyoyin ta ce tuni tawagar da za ta riga Shugaban ta tafi Saudiyyar.

“Ba kamar ziyarar baya ba, wannan ta aiki ce. An kammala komai don yin tafiyar.”, In ji majiyar.

Daga bisani an gano cewa Shugaban zai je Saudiyyar ne don halartar Taron Ƙoli Karo na 14 na Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi, OIC da za a yi a ƙasar.

Taron Ƙolin wanda aka shirya gudanarwa ranar 31 ga watan Mayu zai tattauna a kan “matsalolin da duniya ke fuskanta a halin yanzu da wasu ci gaba da aka samu a wasu ƙasashe mambobin OIC”.

Laƙabin Taron Ƙolin shi ne Together for the Future, kuma Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdul’aziz Al Saud ne zai ɗauki nauyinsa.

An kafa OIC ne a shekarar 1969, kuma tana da ƙasashe mambobi 57.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan