Sabon Gwamnan Adamawa ya fara naɗe-naɗen muƙamai

329

Sabon Gwamnan Jihar Adamawa da ya sha rantsuwar kama aiki jiya, Ahmadu Umaru Fintiri ya naɗa Alhaji Ahmad Bashir a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar, SSG.

Gwamnan ya kuma naɗa Solomon Kumangar a matsayin Darakta Janar, Kafafen Watsa Labarai da Sadarwa.

Wata sanarwa da Babban Sakataren Gudanarwa na Gidan Gwamnatin Jihar, Alhaji Bello Sugu ya fitar ta ce naɗe-naɗen sun fara aiki ne nan take.

Haka kuma, an naɗa wani ɗan jarida mazaunin Yola dake aiki da Gidan Talabijin na AIT, George Kushi a matsayin Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamnan Jihar, Seth Crowther.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan