Sabon Gwamnan Bauchi ya naɗa Sakataren Gwamnati

103

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya amince da naɗin Muhammad Baba a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar, SSG da kuma Dakta Abubakar Kari a matsayin Shugaban Ma’aikatansa, CoS.

Dakta Ladan Salihu, mai magana da yawun Gwamnan ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ranar Alhamis a Bauchi.

Sanarwar ta ce sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Alhaji Bashir Yau, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Mataimakin Gwamna, Baba Tela.

Haka kuma, a cikin naɗe-naɗen akwai Mataimakin Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jaridu na Ƙasa, NUJ, Muktar Gidado wanda aka naɗa a matsayin Mataimaki na Musamman ga Gwamna Kan Kafafen Watsa Labarai, sai Umaruji Hassan a matsayin Chief Protocol.

Naɗe-naɗen za su fara aiki ne daga 30 ga watan Mayu, 2019.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan