Ƙaramar Salla: Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranakun hutu

194

Gwamnatin Tarayya ta bayyana Talata, 4 ga watan Yuni da Laraba, 5 ga watan Yuni, 2019 a matsayin ranakun hutun Bikin Ƙaramar Salla da Musulmi ke yi.

Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Barista Georgina Ekeoma Ehuriah, wadda ta bada sanarwar a madadin Gwamnatin Tarayya, ta taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin Ramadan cikin nasara, ta kuma yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su yi addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai, arziƙi da ɗorewar ƙasar nan.

Ta ja hankalin ‘yan Najeriya da su yi watsi da kalaman ɓatanci da halayen da ka iya raba kan ƙasar nan, su kuma haɗa kai da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen gina Najeriya mai zaman lafiya, mai ƙarfi da haɗin kai don cimma matakin tattalin arziƙi na gaba.

Barista Ehuriah ta ƙara jaddada shirin Gwamnatin Tarayya na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya, tana mai ƙarawa da cewa an umarci jami’an tsaron dake ƙarƙashin Ma’aikatar da su tabbatar da samar isasshen tsaro kafin, yayin da bayan Bikin Ƙaramar Sallar.
Babban Sakatariyar ta nanata buƙatar da Gwamnatin Tarayya ke yi wa ‘yan Najeriya na su ci gaba da riƙo da kyawawan halaye da suka koya a cikin watan Ramadan.

Daga ƙarshe ta taya ‘yan Najeriya murnar Bikin Ƙaramar Salla.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan