Dole Oshimohole ya yi murabus- Shittu

233

Tsohon Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu ya ce jam’iyyar APC ka iya ɓacewa idan Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu, matuƙar Adamawa Oshimohole ya ci gaba da zama shugaban jam’iyyar.

Mista Shittu ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Abuja yayinda yake tattaunawa da manema labarai a wani martani da ya mayar ga wata wasiƙa mai shafi shida da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC (Arewa), Sanata Lawal Shu’aibu ya rubuta wa Oshimohole, inda ya yi kira a gare shi da ya yi murabus.

A cikin wasiƙar da ya aika da ita ranar Talata, Mista Shu’aibu ya yi kira ga Oshimohole da ya yi murabus sakamakon kasa ciyar da jam’iyyar APC gaba tunda ya zama shugabanta.

Ya zargi Oshimohole da rashin cancancta, kama-karya da rashin dattako wajen tafiyar da al’amuran jam’iyyar.

A cewar Mista Shu’aibu, Oshimohole ba shi da cancancta da abubuwan da suka zama wajibi na jam’iyyar.

Ya lura da cewa kima da tagomashin da jam’iyyar APC ta riƙa samu a tsakanin mambobinta da magoya bayanta kafin Oshimohole ya zama Shugaba sun ragu.

“Na goyi bayan Oshimohole ya yi murabus; gaskiyar ita ce indai da Oshimohole, wannan jam’iyya za ta yi ƙasa da zarar Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu.

“Oshimohole yana ji da kansa, kuma yana da babbar matsala, kuma yana so ya mamaye kowane yanayi, kuma dimukuraɗiyya ba haka take ba.

“Mista Shittu ya ce mafiya yawan jiga-jigan jam’iyyar waɗanda ke tunanin gaban jam’iyyar, ci gabanta da ɗorewarta bayan wa’adin mulkin Shugaban Ƙasa, ba sa son Oshimohole ya ci gaba da zama shugaban jam’iyyar.

Ya nanata cewa saboda waɗannan jiga-jigan jam’iyyar sun damu sosai, za su yi duk mai yiwuwa don su tabbatar da cewa Oshimohole ya yi murabus.

Babban Kwamitin Zartarwa na Jam’iyyar APC da Oshimohole ke yi wa jagoranci shi ya hana Mista Shittu yin takarar gwamna a Jihar Oyo.

Dama tunda farko, Mai ba APC shawara kan harkokin shari’a, Babatunde Ogala ya zargi Oshimohole da yi masa katsalandar a aikinsa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan