Gwamnan Bauchi ya bada umarnin a biya ma’aikatan jihar albashi

242

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya umarci Akanta Janar na Jihar da ya biya ma’aikatan jihar bashin albashin da suke bi.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Kan Kafafen Watsa Labarai, Mukhtar Gidado ya sanya wa hannu, ya kuma raba wa manema labarai ranar Juma’a a Bauchi.

A cewar sanarwar, Gwamnan ya bada umarnin biyan albashin ma’aikatan ne don rage musu raɗaɗin da suke ciki.

Sanarwar ta umarci a fara biyan ma’aikatan daga yau Juma’a, 31 ga watan Mayu zuwa Litinin, 3 ga watan Yuni, 2019.

Amma Gwamna Mohammed ya ce ba za a biya ma’aikatan da gwamnatin da ta gabata ta ɗauka a watan da ya gaba ta ba.

“Akanta Janar zai tabbatar da cewa duk mutanen da aka ɗauka aiki a watan Afrilu da Mayu ba a biya su ba”, sanarwar ta yi gargaɗi.

Gwamnan ya nanata shirin gwamnatinsa na kula da jin daɗin ma’aikata a matsayin abinda gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kai.

Daga nan sai ya yi kira ga ma’aikata a jihar da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu don samun aikin gwamnati mai inganci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan