Majalisar Dokokin Ogun ta sauke dukkan sarakunan da tsohon gwamna ya naɗa

291

A ranar Juma’a ne Majalisar Dokokin Jihar Ogun ta amince da wani ƙudiri da zai sauke dukkan Sarakunan Gargajiya da aka naɗa daga watan Fabrairu, 2019 har zuwa 28 ga watan Mayu, 2019.

Tsohon gwamnan jihar, Ibikunle Amosun ne ya naɗa sarakunan, ba tare da al’umma suna so ba.

Naɗa sarakunan ya jawo ka-ce-na-ce a jihar, musamman a yankin Aworiland, inda ake da ƙorafe-ƙorafen cewa an naɗa waɗanda ba ‘yan asalin jihar ba a matsayin sarakuna.

Haka kuma ranar Juma’a Majalisar Dokokin ta dakatar da waɗanda aka naɗa muƙamai a matakan ƙananan hukumomi.

A cewar Majalisar, ta yi hakan ne don samun damar binciken zargin rashin ɗa’a da kashe kuɗaɗen gwamnati ba bisa ka’ida ba da ake yi musu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan