Alamomi shida na Daren Lailatul Ƙadari

205

Daren Lailatul Ƙadari yana da alamomi da ake gane shi da su, waɗannan alamomi suna kasancewa ne a cikin Daren Lailatul Ƙadarin.

1- Dare ne mai haske, babu zafi ko sanyi a cikin sa.

An karbo daga Jabir Ɗan Abdullahi (Allah Ya ƙara yadda a gare shi) ya ce:

“Haƙiƙa ni an nuna min Daren Lailatul Ƙadari, sannan an mantar da ni shi, yana goman ƙarshe na Ramadan, dare ne da babu sanyi ko zafi a cikin sa, kuma mai haske ne” (Ibn Khuzaima).

2- Rana tana fitowa da safiyar daren fara tas.

Lokacin da aka tambayi Ubayyu Ɗan Ka’ab (Allah Ya ƙara yadda a gare shi) a kan alamomin Daren Lailatul Ƙadari, sai ya ce: “Alamar da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) ya ba mu labari ita ce, rana tana ɓullowa, wannan rana babu haske a tare da ita” (Tirmizi).

3- Yanayi zai canza ya zama mai daɗi, za a ji iska mai daɗi, nitsatssiya” (Ibn Khuzaima da Dayalisi).

4- Samun nutsuwar zuciya da kimtsuwa, da kuma farin ciki da samun jin daɗin ibada (annashuwa).

5- Za ka iya ganin shi (Lailatul Ƙadari), a mafarki, kamar yadda sahabbai suka gani.

  • Za a iya yin mafarkin ga shi ana ibada a cikin daren.

6- Rana za ta fito babu zafi (idan lokacin zafi ne) (Muslim).

Waɗannan su ne alamomin da ake gane Daren Lailatul Ƙadari. Amma cewa da ake itatuwa za su faɗi su yi sujjada, rana za ta kusanto (ƙasa-ƙasa), taurari za su kusanto (ƙasa-ƙasa), karnuka za su daina kuka, wannan tatsuniya ce aka ƙaga a cikin addini, wanda kuma ba gaskiya ba ne.

Allah Ya datar da mu da wannan garaɓasa. Ameen.

Ɗan uwanku

Abdurrahman Abubakar Sada

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan