Ko kun san lambobin wayar da za ku tuntuɓa idan kun ga jinjirin watan Shawwal?

235

Majalisar Sarkin Musulmi ta buƙaci al’ummar Musulmin ƙasar nan da su fara duban jinjirin watan Shawwal daga yau Litinin, 29 ga watan Ramadan.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Kwamitin Ganin Wata na Ƙasa, Yahaya M Boyi ya fitar ranar Lahadi.

“Majalisar Sarkin Musulmi na son tunatar da ku cewa gobe (yau) Litinin, 3 ga watan Yuni, 2019, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Ramadan, 1440 ita ce rana ta farko da za a duba watan Shawwal, 1440. Idan an ga watan, sai ku sanar da Majalisar ta waɗannan lambobi:

08037157100, 08065480405. 08035965322, 08039655007, 08066303077, 08030413534″, in ji sanarwar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan