Yadda ake yin Zakkar Fidda Kai

330

Zakkar Fidda Kai zakka ce da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) ya wajaba ta a kan dukkan Musulmi, ɗa ko baiwa, yaro ko babba.

“Ɗan Umar (Allah Ya ƙara yadda a gare shi) ya ce: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) ya farlanta Zakkar Fidda Kai a kan kowane Musulmi, bawa, ɗa, mace ko namiji, yaro do babba tsakanin Musulmi, Sa’i ɗaya na busasshen dabino ko Sa’ai ɗaya na Sha’ir”.

Yaushe ake fitar da ita?

Ana fitar da Zakkar Fidda Kai ne kafin a je Sallar Idi. Za a iya fitar da ita ranar 28 ko 29 ga Ramadan. Ana ma iya fitar da ita ranar Salla, kafin a je masallaci.

Me ake yin Zakkar Fidda Kai da shi?

Ana yin Zakkar Fidda Kai ne da abincin da al’umma suka fi ci. Misali, mu a nan sai mu ce shinkafa, masara, dawa da sauransu.

Waya zai bada ita?

Duk Musulmin da yake da fiye da abinda zai ci, ya dogara da kansa zai fitar da ita. Shugaba zai bayar da ita a madadin waɗanda suke ƙarƙashinsa.

Su wa ake ba?

Ana ba mabuƙata waɗanda ba su da abinda za su ci.

Da me ake yin amfani wajen bayar da ita?

Ana yin amfani da Mudun Nabiyyi a wajen auna abinda za a bayar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan