Dalilin da yasa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano ke son a dakatar da Sarki Sanusi

197

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano ta bada shawarar dakatar da Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II biyo bayan zargin karkatar da Naira Biliyan 3.4 da take yi wa Sarkin.

Ana zargin an kashe waɗannan kuɗaɗe ne tsakanin shekarar 2014 da 2017.

Hakan na ƙunshi ne a cikin wani rahoton bincike da Hukumar ta gudanar, wanda shugabanta, Muhuyi Magaji ya sanya wa hannu, aka kuma ba Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN kwafi ranar Litinin a Kano.

A cewar rahoton, an gudanar da binciken ne sakamakon ƙorafi da aka yi game da yadda Masarautar Kano ke kashe kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba a ƙarƙashin Sarki mai ci.


Rahoton na wucin gadi ya kawo batutuwa huɗu masu muhimmanci da suka haɗa da zargi, jimillar kuɗaɗen da ake zargi, katsalandar wajen bincike da shawarwari.

Rahoton ya nuna cewa Masarautar Kano ta kashe fiye da Naira Biliyan 1.4 a abubuwa da dama da aka yi imanin da akwai ɗungushe.

Haka kuma, ana zargin Majalisar Sarkin da kashe fiye da Naira Biliyan 1.9 da ba ta yi bayanin yadda ta kashe su ba, bisa buƙatun da ake ganin na ƙashin kai ne, wanda ya bada jimillar kuɗaɗen da ake zargi a kansu.

A cewar rahoton, wannan kashe-kashen kuɗaɗe ya saɓa da Sashi na 120 na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasar nan na 1999, da kuma Sashi na 8 na Dokar Asusun Musamman na Majalisar Masarautar Kano ta 2004.

Haka kuma, kashe-kashen kuɗaɗen ya saɓa da Sashi na 314 na Penal Code da tanade-tanaden Sashi na 26 na Dokar Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano ta 2008 (da aka yi wa kwaskwarima).

“Yana kuma cikin ra’ayin wannan Hukumar, bisa hujjar da ake da ita, cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya riƙa yin katsalandar wajen binciken ta hanyoyi da dama, waɗanda suka haɗa da hana jami’an da Hukumar ta gayyata don yin ƙarin haske amsa gayyatarta.

“Wannan abu yana shafar aikin da doka ta sa mu sosai, ya kuma saɓa da tanade-tanaden Sashi na 25 na Dokar da ta ba Hukumar ta 2008 (da aka yi wa kwaskwarima)”.

Sakamakon haka, sai rahoton ya bada shawarar cewa a dakatar da babban wanda ake zargi, wato Muhammadu Sanusi II da dukkan sauran waɗanda ake zargi, har sai an gama bincike.

“Wannan aiki ne na gudanarwa da ya zama wajibi, da yake nufin a hana waɗanda ake zargi ci gaba da tsoma baki a binciken da Hukumar ke yi.

‘Hukumar tana kuma bada shawarar cewa a ƙwace kwangilar da aka ba kamfanin Tri-C Nigeria Limited ta yi wa Babban Ɗaki, Ƙofar Kudu da Gidan Sarki Ɗorayi kwaskwarima saboda kamfanin na ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi ne, wato Alhaji Mannir Sanusi, (Shugaban Ma’aikatan Sarkin)”, a cewar rahoton.

Rahoton ya ce kamfanin ya gaza biyan ƙaramin kamfanin da aka ba kwangilar, Cardinal Architecture Ltd bayan an biya shi kuɗin daidai.

Hukumar ta ƙara bada shawarar cewa a ba hukumomin da suka dace damar kula da yadda Majalisar Sarki ke gudanar da al’amuranta kamar yadda dokoki da manufofi suka tanada, har sai Hukumar ta fitar da sakamakon bincike na ƙarshe.

Ta kuma ƙara bada sanarwar cewa a ɗauki matakin shari’a akan waɗanda ake zargi, har lokacin da za a fitar da sakamakon bincike na ƙarshe, da kuma bada shawara ta shari’a.

Har yanzu Fadar Sarkin Kano ba ta mayar da martani ga wannan sabon binciken ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan