Jawabin Sarki Sanusi a yayin Sallar Idi

243

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi kira da a ilmantar da ‘ya’ya mata.

Sarkin ya yi kiran ne yayinda yake jawabi jim kaɗan bayan ya yi limancin Sallar Idi a Babban Filin Idi na Ƙofar Mata ranar Talata.

Ya yi kira ga shugabannin siyasa a dukkan matakai da su bada fifiko ga Ilimin mata kamar yadda suke ba na maza.

“Akwai buƙatar su bada ƙoƙarinsu wajen ilimin mata kamar yadda suke ba takwarorinsu maza”, in ji Sarkin.

Ya jaddada buƙatar da ake da ita na ‘yan Najeriya su yi addu’ar samun zaman lafiya da ci gaban jihar Kano da ƙasar nan gaba ɗaya.

Basaraken ya kuma yi kira ga Musulmi da su ji tsoron Allah a cikin al’amuransu, yana mai tunatar da su cewa kowane ɗayansu zai yi bayanin abubuwan da ya aikata a ranar gobe.

Sarkin ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da yin addu’a bisa kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran bala’o’i.

Ya yi kira ga al’ummar Kano da su yi aiki a matsayin al’umma ɗaya domin ci gaban jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya ruwaito cewa waɗanda suka halarci Sallar Idin a Babban Filin Idin na Ƙofar Mata sun haɗa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Mataimakinsa, Nasiru Gawuna da Sakataren Gwamnatin Jihar, Usman Alhaji.

Sarki Sanusi yana yin jawabinsa na farko ne kwana ɗaya bayan Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano ta yi masa zargin cin hanci, ta kuma bada shawarar a dakatar da shi.

Hukumar ta ce ta gano fiye da Naira Biliyan 3.4 da take zargin Sarki Sanusi ya kashe ba bisa ka’ida ba.

Ta ce na kashe kuɗaɗen ne tsakanin shekarar 2014 da 2017.

Sarki Sanusi bai mayar da martani game da zargin ba, wanda ke zuwa makonni bayan Gwamnatin Jihar Kano ta gididdiba Masarautar zuwa gida huɗu.

Gwamnatin Jihar dai ta ƙaryata cewa matakin yana da dangantaka da siyasa.

NAN ya ce an tsaurara tsaro yayin gudanar da Sallar Idin, an jibge jami’an ‘yan sanda dauke da makamai da sauran jami’an tsaro a filayen Idi daban-daban don gudanar da bikin Salla cikin lumana.
Haka kuma daga cikin waɗanda suka halarta akwai hakimai da ‘yan Majalisar Sarki.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan