Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da Hawan Nasarawa

177

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya rubuta wa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II wasiƙa, inda yake bayyana cewa ba zai iya halartar manya-manyan Haye-hayen Salla da Masarautar Kano ke shiryawa lokacin bukukuwan Salla ba.

A wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 4 ga watan Yuni, 2019 wadda Ibrahim Hamza, Daraktan Ayyuka na Musamman, Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano ya sanya wa hannu, Gwamnan ya ce rashin halartar tasa yana da dangantaka da wasu ayyuka da suka yi masa yawa.

“An umarce ni da in Sanar da kai cewa, Mai girma Gwamna, Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abudullahi Umar Ganduje, OFR ba zai iya halartar Hawan Daushe na wannan shekarar ba sakamakon wasu ayyuka da suke buƙatar cikakkiyar kulawarsa. Haka kuma, an dakatar da Hawan Nasarawa da aka saba yi duk ranar uku ga Salla da ake zuwa Gidan Gwamnati saboda wasu dalilai.

“Yayinda muke baƙin cikin irin rashin jin daɗi da wannan abin ka iya jawo wa Majalisar Sarki, muna fata Maimartaba, Sarki zai yi bukukuwan Salla cikin nasara”, in ji wasiƙar.

Dangantaka tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi ta yi tsami biyo bayan goyon baya da ake zargin Sarkin ya ba ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf a zaɓen da ya gabata. Tare da sukar wasu daga cikin manufofi marasa amfani da ma’ana da Gwamnatin ta Gandujen ke bullowa da su da Sarkin yake yi wanda hakan bai yiwa Gwamnatin Kanon Dadi.

A wani salo da ake ganin na rage ƙarfin Sarki Sanusi ne, Gwamnan ya ƙirƙiri sabbin masarautu huɗu a Bichi, Rano, Gaya da Ƙaraye, inda kowace masarauta aka naɗa mata sabon Sarki. Sai dai Gwamnan Gandujen ya musammanta haka inda ya dage kan cewa don cigaban jama’ar Kano akayi hakan.

Duk da kotu ta hana Gwamnan haka, ya yi watsi da umarnin na kotu, inda ya ba sabbin sarakunan takardun kama aiki da Sandunan Girma.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan