Sanata Danjuma Goje ya janye daga takarar Shugabancin Majalisar Dattijai, ya kuma bayyana goyon bayansa ga takarar Jagoran Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan.
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya bayyana haka bayan tattaunawar sirri da Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja ranar Alhamis.
Da yake yi wa Manema Labarai dake Gidan Gwamnati jawabi, Gwamna El-Rufa’i ya ce an gama da wannan batu, tunda Sanata Danjuma Goje ya bayyana goyon bayansa ga takarar Sanata Ahmad Lawan.
“Mun tattauna matakan da za mu kawo haɗin kai a Shugabancin Majalisar Dokoki ta Ƙasa, mun fara da Majalisar Dattijai.
“Ina mai farin cikin sanar da cewa Maigirma Sanata Goje ya yadda ya goyi bayan, ya kuma tallafi zaɓin jam’iyya da kuma zaɓin Shugaban Ƙasa a Majalisar Dattijai, wato Sanata Ahmad Lawan.
“Mun gode wa Sanata Goje sosai bisa sadaukarwarsa da haƙurinsa. An daɗe ana wannan tattaunawar, kuma ina ganin an girmama ni da na zama daga ciki, kuma na gode masa sosai da ya duba yawan shekarun da muka yi aiki tare lokacin da yake Minista.
“Na san shi mutum ne mai dattaku sosai, kuma mutum ne mai cika alƙawari, na ji daɗi da ya zo ya ga Shugaban Ƙasa don a gama wannan magana lokaci ɗaya”, in ji Gwamna El-Rufa’i.
Sanata Goje ya ce: “Da farko, ina so in yi amfani da wannan dama in gode wa Allah da ya ba ni wannan damar yau. Ina so in gode wa magoya bayana, abokan siyasata a dukkan faɗin ƙasar nan waɗanda suka yi ta kira gare ni da in yi takarar Shugaban Majalisar Dattijai, na saurare su, kuma na gode musu sosai.
“Ina son in ce a matsayina na dattijo a Majalisar Dattijai lokaci mai tsawo, a shekaruna, ya kamata in yaba da irin shugabancin da yake zuwa daga manyanmu. To, duk da waɗannan kiraye-kirayen, duk da goyon bayan da nake da shi a tsakanin abokan aikina a Majalisar Dattijai, na yanke shawarar, saboda biyayyar da nake yi wa Shugaban Ƙasa, kuma saboda biyayyar da nake yi wa jam’iyyar APC, don ci gaban jam’iyyarmu kuma don ci gaban ƙasa, don in taimaki Shugaban Ƙasa ya cika alƙawuransa, na yanke shawarar zan girmama buƙatarsa, ba zan yi takarar Shugaban Majalisar Dattijai ba.
“Maimakon haka, zan goyi bayan matsayin jam’iyya, zan mara wa takarar Sanata Ahmad Lawan baya”, in ji shi.
Da aka tambaye shi ko wannan matakin ya zama ƙaƙabe, sai ya ce: “Ba na tunanin ƙaƙabe ne. Ba tilasta min aka yi in janye ba. Kawai na faɗa muku cewa a shekaruna, ina da damar da zan yi tunani sosai, in girmama manya, in girmama jam’iyyata.