Ganduje na dab da dakatar da Sanusi

Gwamnatin Jihar Kano ta buƙaci Sarkin Kano Muhammad Sanusi II ya yi bayanin yadda Masarautar Kano ta kashe Naira Biliyan 3.4 a ƙarƙashin shugabancinsa.

Gwamnatin Jihar Kanon ta buƙaci Sarkin ya yi bayanin ne a cikin wata wasiƙa da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ya sanya wa hannu, mai ɗauke da kwanan watan 6 ga watan Yuni, 2019.

“Gwamnatin Jihar Kano ta karɓi wani rahoto daga Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano, mai ɗauke da kwanan watan 31 ga watan Mayu, 2019, kamar yadda muka sa kwafin rahoton a nan a ci gaba da binciken da Hukumar ke kan yi da ya haɗa da kashe Naira Biliyan 3.4 da Majalisar Masarautar Kano ta yi ba bisa ka’ida ba a ƙarƙashin shugabanka daga shekarun 2014 zuwa 2017. Rahoton ya bayyana ɓangarorin zargin da shawarwari kamar yadda yake a shafi na 14 zuwa na 16 a ciki.

“Sakamakon haka, a cikin wannan rahoto da ake magana, Hukumar ta bada shawarar a dakatar da kai da dukkan sauran waɗanda ake zargi dake da alaƙa da batun har zuwa lokacin da sakamakon binciken zai fito, don kuma a ba ta damar yin bincike ba tare da katsalandan ba.

“Duba da wannan batu da aka kawo a sama, ina buƙatar ka da ka yi gamsasshen bayani cikin sa’o’i 48 da karɓar wannan wasiƙa don ba Gwamnati damar ɗaukar matakin da ya dace kan batun cikin gaggawa”, a cewar wasiƙar.

Da aikawa da wannan wasiƙa, ana iya cewa tsamin dangantaka tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Masarautar Kano ya ƙara fitowa fili.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan