Soke Hawan Nasarawa: Masarautar Kano ta Mayar da Martani

166

Masarautar Kano ta ce za ta yi biyayya ga umarnin gwamnati na soke Hawan Nasarawa.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Muƙaddashin Sakataren Masarautar, Alhaji Abba Yusuf ya sanya wa hannu ranar Laraba.

“Dangane da umarni da aka samu daga Gwamnatin Jiha na cewa kada Masarautar Kano ta yi Hawan Nasarawa na wannan Ƙaramar Sallah, ana sanar da hakimai da dukkan jama’a cewa an janye hawan domin bin umarnin Gwamnati.

“Haka kuma bisa rahoto da Masarautar Kano ke samu cewa akwai wasu ɓata gari da suke shirin tada hankalin jama’a ta kowane hali, Masarautar ta ga ya dace ta soke Hawan Ɗorayi don gudun fitina.

“A madadin Hawan Ɗorayi wanda zai faɗo ranar Juma’a (7 ga Yuni, 2019), Masarautar Kano na gayyatar dukkan limamai da malamai da sauran jama’a domin yin addu’a ga marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, wanda Allah Ya yi wa rasuwa shekara biyar da suka wuce, tare da godiya ga Allah da Maimartaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya cika shekara biyar a kan sarautar Kano. Za a yi wannan addu’a ne a Babban Masallacin Juma’a na Cikin Birni da ƙarfe 8 na safe idan Allah Ya kai mu.

“Masarautar na godiya ga jama’a bisa addu’o’i na alheri da soyayya da ake nuna wa wannan Masarauta. Masarautar na kira da babbar murya cewa a ci gaba da addu’o’i na zaman lafiya, kuma jama’a su zauna lafiya da junansu.

“Muna ƙara addu’a Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya da ci gaba mai albarka a wannan jiha da ƙasa baki ɗaya”, a cewar sanarwar.

Dangantaka dai ta yi tsami tsakanin Gwamna Ganduje da Masarautar Kano, biyo bayan zargin da ake yi cewa Sarki Sanusi ya goyi bayan ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf a zaɓen gwamna da ya gabata.

Hakan ne yasa Gwamnatin Jihar ta Kano ta ƙirkiro sabbin masarautu huɗu a Bichi, Gaya, Ƙaraye da Rano, ta kuma naɗa sabon sarki a kowace masarauta, wani abu da ake yi kallon rage ƙarfin Sarki Sanusi ne.

Amma Gwamnatin Jihar ta sha nanata cewa ƙirƙirar sabbin masarautun ba shi da danganta da siyasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan