Yadda wasu manya suka sasanta Ganduje da Sarki Sanusi

201

An sasanta rikicin dake tsakanin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II biyo bayan wani taron sulhu da aka yi tsakanin su ranar Juma’a a Abuja.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna Ganduje, Abba Anwar ya fitar, aka kuma ba Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ranar Asabar.

A cewar Mista Anwar, shahararren ɗan kasuwar nan na Jihar Kano, Alhaji Aliko Dangote da Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, AGF, Gwamnan Jihar Ekit, Dakta Kayode Fayemi ne suka ya dalilin taron sulhun.

Ya ce bayan taron, mutanen biyu sun gaisa da juna ranar Juma’a a Abuja.

“Lokacin da shugabannin biyu suka haɗu, sun taya juna murnar kammala azumin watan Ramadan da kuma murnar bukukuwan Ƙaramar Salla.

“Dukkan shugabannin biyu sun yi jawabai, sun kuma yi kira ga dukkan Musulmi da su ci gaba da yin amfani da kyawawan abubuwan da suka koya a cikin watan Ramadan.

“Sarki Sanusi ya yi amfani da damar wajen taya Gwamna Ganduje murnar samun nasarar wa’adin mulkinsa na biyu. Ya kuma yi wa Gwamnan fatan yin mulki cikin nasara”, in ji Mista Anwar.

A cewar sanarwar, mutanen biyu sun yadda da cewa don samun lafiyayyiyar dagantaka tsakanin cibiyoyin gwamnatin guda biyu da Majalisar Masarautar Kano, za a ci gaba da tattaunawar.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Alhamis ne Gwamnatin Jihar Kano ta aika da Takardar Neman Bahasi zuwa ga Sarki Sanusi bisa zargin sa da yin bushasha da Naira Biliyan 3.4 na Majalisar Masarautar Kano.

Da wannan sulhu, ana iya cewa an kawo ƙarshen takun-saƙar da aka daɗe ana samu tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan