Zargin kashe kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba: Sarki Sanusi ya mayar da martani

171

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya mayar da martani game da zargin da Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano ta yi masa cewa ya kashe Naira Biliyan 3.4 na Majalisar Masarautar Kano ba bisa ka’ida ba daga shekarar 2014 zuwa 2017.

Sarkin ya mayar da martanin ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 7 ga watan Yuni, 2019 wadda Muƙaddashin Sakataren Majalisar Masarautar Kano, Abba Yusuf ya sanya wa hannu.

A cewar wasiƙar, lokacin da aka naɗa Sarki Sanusi II, abinda ya samu a lalitar Majalisar Masarautar Kano shi ne 1,893,378,927.38 (Naira Biliyan Ɗaya da Miliyan Ɗari Takwas da Casa’in da Uku, da Dubu Ɗari Uku da Saba’in da Takwas, da Ɗari Tara da Ashirin da Bakwai da Kwabo Talatin da Takwas).

Wasiƙar ta ƙara da cewa Sarkin Kano ba shi ne Akanta na Majalisar Masarautar Kano ba, shi Sakataren Majalisar ne.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 6 ga watan Yuni ne Gwamnatin Jihar Kano ta aika da Takardar Neman Bahasi game zuwa ga Sarki Sanusi II, inda ta ba shi awa 48 da ya mayar da martani game da zargin kashe kuɗaɗen.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan