Majalisar Dokokin Jihar Kano ta zaɓi sabon Kakaki

193

A ranar Litinin ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta zaɓi mamba mai wakiltar Mazaɓar Ɗan Majalisar Jiha ta Ajingi, Abdul’aziz Garba Gafasa a matsayin sabon Kakakin Majalisar

Tuni aka rantsar da shi tare da Mataimakinsa, Hamisu Chidari.

Mista Gafasa, wanda gogaggen ɗan majalisa ne, an fara zaɓar sa a matsayin Kakakin Majalisar ne daga shekarar 2007 zuwa 2011, lokacin wa’adin mulkin tsohon Gwamnan Jihar Kano na biyu, Malam Ibrahim Shekarau.

Jam’iyyar APC ce dai ke da rinjaye a Majalisar, inda take da ‘yan majalisa 27, yayinda jam’iyyar PDP ke da 13.

Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abudullahi Umar Ganduje ne ya mara wa Mista Gafasa baya a wani taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki da aka yi a Gidan Gwamnatin Jihar Kano ranar Asabar da daddare.

Koda yake dai tsagin tsohon Kakakin Majalisar, Alhassan Rurum ya tsayar da ɗan mamba mai wakiltar Mazaɓar Ɗan Majalisar Jiha ta Doguwa, Salisu Doguwa, Gwamnan ya fi ƙarfin su, inda ya tsayar da Mista Gafasa.

Haka kuma, Gwamnan ya mara wa mamba mai wakiltar Mazaɓar Ɗan Majalisar Jihar ta Makoɗa, Hamisu Chidari a matsayin Mataimakin Kakakin Majalisar, kamar yadda ya goyi bayan Labaran Abdul Madari, mai wakiltar Mazaɓar Ɗan Majalisar Jiha ta Warawa a matsayin Shugaban Masu Rinjaye.

Sauran waɗanda Gwamna Ganduje ya mara wa baya su ne mamba mai wakiltar Mazaɓar Ɗan Majalisar Jiha ta Ƙiru, Kabiru Dashi a matsayin Bulaliyar Majalisa; mamba mai wakiltar Mazaɓar Ɗan Majalisar Jiha ta Kura/Garun Mallam, Hayatu Ɗorawar Sallau a matsayin Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye; da wani mamba mai wakiltar Mazaɓar Ɗan Majalisar Jiha ta Kabo, Ayuba Labaran Alhassan, a matsayin Mataimakin Bulaliyar Majalisa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan