Ranar Dimukoraɗiyya: Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar hutu

211

A ranar Litinin ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana Laraba, 12 ga watan Yuni, 2019 a matsayin ranar hutu don yin bukukuwan Ranar Dimukoraɗiyya ta Ƙasa.

Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Georgina Ehuriah ta bayyana haka a madadin Gwamnatin Tarayya a cikin wata sanarwa da Mohammed Manga, Daraktan Yaɗa Labarai da Huɗɗa da Jama’a na Ma’aikatar ya sanya wa hannu ranar Litinin a Abuja.

Wannan mataki na Gwamnatin Tarayya ya biyo bayan gyara Dokar Ranar Dimukoraɗiyya da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta yi, inda ta mayar da 12 ga watan Yuni na kowace shekara a matsayin Ranar Dimukoraɗiyya, maimakon 29 ga watan Mayu da aka sani a baya.

Misis Ehuriah ta taya dukkan ‘yan Najeriya na gida da na waje murnar kafuwar Mulkin Dimukoraɗiyya a Najeriya.

Babbar Sakatariyar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yin koyi da irin sadaukarwa da jaruman dimukoraɗiyya na ƙasar nan suka yi.

Ta jaddada cewa ba za a taɓa mantawa da waɗanda suka rasa rayukansu wajen tabbatar da Mulkin Dimukoraɗiyya a Najeriya ba.

Misis Ehuriah ta ƙara yin kira ga ‘yan Najeriya da su su haɗa kai da Shugaba Muhammadu Buhari don ci gaban ƙasar nan.

Daga ƙarshe ta taya dukkan ‘yan Najeriya na gida da na waje Murnar Ranar Dimukoraɗiyya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan