Yadda sanatoci 107 suka zaɓi Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai

295

Sanata Ovie Omo Agege ya yi nasarar zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai ta Tara.

Sanatan, mai wakiltar Delta ta Tsakiya ɗan jam’iyyar APC mai mulki, ya kayar da abokin karawar sa, Ike Ekweremadu, tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, ɗan jam’iyyar PDP.

Sanata Omo Agege ya yi samu ƙuri’a 69, yayinda Sanata Ekweremadu ya samu ƙuri’a 38.

Muƙamin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai shi ne muƙami na biyu mafi girma a Majalisar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan