Bikin Ranar Dimukuradiyya: Shugaba Buhari Ya Canza Wa Babban Filin Wasa Da Ke Abuja Suna

A yayin da ake gudanar da bikin ranar damakaradiyya wanda ya kasance karo na farko a yau, a filin Eagle Square da ke Abuja, shugaba Buhari ya sanar da al’ummar kasa cewa ya sauya sunan babban filin wasa na Abuja zuwa sunan marigayi Mashood Abiola.

Wannan Batu yayi wa mutanen da ke zaune a wannan fili dadi ganin yadda wurin ya barke da tafi bayan sanarwan na shugaban kasa.

Marigayi Mashood Abiola, shi ne dan takarar da ake sa ran yaci zaben shugaban kasa a shekarar 1993 amma sai gwamnatin soja na wannan lokaci karkashin mulki Gen Ibrahim Badamasi Babangida ta soke zaben.

Wannan Dalili ya sa shugaba Buhari ya aiyya wannan rana ta 12 ga watan Yuni a matsayin ranar damakaradiyya domin tunawa da rage radadin faruwar lamarin a bara kuma aka gudanar da bikin karo na farko a yau.

Baya ga Haka, a cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Buhari ya ce kasar nan zata iya samun cigaba kamar kasashen china da India, da Indonesia, inda ya ce babu wani abu da zai hana mu mu kai ga gaci.

Bikin na yau, ya samu halartar shugabanin kasashen Chad, da Gambia, da Niger da Rwanda. Sai sabbin shugabanin Majalisun dokoki na Tarayya, da manyan Jami’an Gwamnati, da manyan baki daga ciki da wajen kasar nan.

Amma kuma babu ko da daya daga cikin tsofaffin shugabannin kasarnan da ya hallarci taron, sannan kuma babu wani da

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan