Bangarorin Da Gwamnatin Buhari Zata Maida Hankali Akai A Wa’adinta Na Biyu

281


A yayin da ya ke gudanar da jawabi a filin taro na Eagle Square da ke Abuja a jiya laraba, 12 ga watan Yuni, shekarar 2019, shugaban kasa Muhammad Buhari ya tattauna akan wasu fannoni na rayuwa da gwamnatinsa zata maida hankali a kai domin kawo cigaba ga rayuwar al’umma a wa’adinsa na biyu.

Shugaban, wanda bai yi wani takamaimen alkawari ga yan kasa ba, ya ce gwamnatinsa zata tabbatar da, ta dora akan ayyukan cigaba da ta fara a baya, a bangarori dabam-dabam.

Sannan ya yi kira ga yan kasa, inda ya bada tabbacin samar da hadin kai a Kasar nan tare da yiwa kowanni bangare adalci.

Shugaba Buhari ya kara da cewa gwamnatinsa zata inganta harkokin kiwon lafiya a dukkanin matakan gwamnati, tare da tallafawa kananan masana’antu, da bayar da tallafi ga masu zuba jari.

Bugu da kari, gwamantinsa zata maida hankali wurin ginin hanyoyi na tsawon kilomita 2000, da gina saura hanyoyi na ruwa, da tituna, da layin dogo, domin agaza wa ‘yan kasuwa da manoma.

Kafin wannan batu, shugaba Buhari ya bayyana nasarori da gwamnatinsa ta samu a wa’adinta na farko wanda suka hadar da; inganta harkokin tsaro, da yaki da cin hanci da rashawa, da Bunkasa tattalin arziki, da samar da aiyukan ci gaban kasa, da samar da aiyukan yi, da yaki da talauci, da gyare-gyare ga kurakuren gwamnatocin baya da sauransu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan