Babban Sakataren Fadar Gwamnatin Tarayya, Jalal Arabi ya roƙi al’umma da su yi watsi da sanarwar dake zagayawa a halin yanzu dake cewa ana ɗaukar ma’aikata a Asibitin Fadar Gwamnatin Tarayya.
Mista Arabi ya bayyana haka ne a wata sanarwa da Attah Esa, Mataimakin Daraktan Sashin Yaɗa Labarai ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Babban Sakataren ya shawarci al’umma da su yi kaffa-kaffa da irin wannan sanarwa, wadda wasu mugaye ke shiryawa don cutar masu neman aiki.
Mista Arabi ya tabbatar da cewa za a binciki tare da gurfanar da waɗanda suka ɗauki nauyin wallafa waccan sanarwa a kotu.
Turawa Abokai