Himma Bata Ga Raggo: Karanta Yunƙurin CITAD na Daƙile Rashin Kammala Aiyuka

235

A yau ne Cibiyar Fasahar Sadarwa da bunƙasa cigaban al’umma wato CITAD ta karrama zakakuran matasa guda shida daga manyan makarantu daga fadin kasar nan.


Mallam Isa Garba na kungiyar ta CITAD ne ya bayyana haka a babban ofishin su da ke birnin Kano.


Matasan dai sun samu nasarar lashe gasar a karo na biyar a fanin rubuta rahoto kan aiyukan da ba a kammala ba a fadin kasar nan, abin da cibiyar ta ke yaki da shi haikan domin su samu kammaluwa ta hanyar Jan hankalin masu zartar da doka da hukunci, a dayan bangaren gasar kuma shi ne Samar da shawara a kan yadda za a dakile cin hanci da rashawa a daukacin kasar nan.

Layusa Jafar Na Karbar Kyauta


Wadanda suka samu nasarar lashe gasar sun hada da Surraya Jamilu daga Jami’ar Jiha ta Yobe, Aisha Inuwa Idris daga Makarantar Fasahar Kiwon Lafiya ta Kano da Idris Nuhu Gaya na Jami’ar Ibadan da ke Jihar Oyo.
Sanan a fanin hanyar yadda za’a dakile rashawa kuma Layusa Jafar Ahmad ta Jami’ar Karatu daga Gida ta kasa ce ta lashe na daya, Rukkaya Ibrahim daga kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya da ke Gumel ta biyu sai kuma na uku Abdullahi Suleman Sani daga Jami’ar Jiha dake Bauchi.


Malam Sani ya bayyana cewa dukan daliban manyan makarantu ka iya shiga gasar, wadda masana zasu tantance su zabi wadda suka yi fice domin samun kyautuka a gasar. Wadanda ke nesa kuma na iya turo wakilan su domin karba masu kyautar a madadin su.

Idris Nuhu Gaya Na Karbar Kyauta


Kyautar dai dubu 30,000, 20,000 da 10,000 ne za a bama na daya, na biyu da na uku. Kuma a halin yanzu har an bude gasar ta wanan watan na Yuni kuma za a rufe ta a talatin ga watan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan