Jami’ar Jihar Ekiti ta ba Sarki Sanusi muƙami

41

Jami’ar Jihar Ekiti ta naɗa Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a matsayin Jagoran Jami’ar, wato Chancellor.

A wata wasiƙa da Matawallen Kano, Aliyu Ibrahim ya aika wa Sakataren Gwamnatin Jihar Ekiti, ya bayyana jin daɗi ga Gwamnan Jihar bisa samun Sarki Sanusi II a matsayin wanda ya dace a naɗa Jagoran Jami’ar Jihar Ekiti.

Sanarwar ta ce Sarki Sanusi zai kawo dukkan wata gogewa da yake da ita domin ciyar da jami’ar gaba.

Dama dai Sarki Sanusi shi ne Jagoran Jami’ar Benin dake Jihar Edo da Jami’ar Skyline ta Najeriya, jami’ar ƙasa da ƙasa mai zaman kanta, irinta ta farko a Arewa Maso Yammacin Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan