Biyo bayan ba tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha Takardar Shaidar Lashe Zaɓe da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta yi, Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Ahmad Lawan ya rantsar da sabon sanatan.
A ranar Alhamis ne sabon Shugaban Majalisar Dattijan ya gabatar da aikinsa na farko, inda ya rantsar da Mista Okorocha, wanda zai wakilci Mazaɓar Sanata ta Imo ta Yamma a Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Mista Okorocha ya sha Rantsuwar Kama Aikin ne a zauren Majalisar da misalin ƙarfe 10:39 na safe, bayan nan kuma, ya sanya wa wasu takardu hannu.
Daga nan sai ya tafi kai-tsaye zuwa wajen Shugaban Majalisar Dattijan, inda suka gaisa.
A ranar Talata ne INEC ta ba Okorocha Takardar Shaidar Lashe Zaɓe bayan an sha taƙaddama a kotuna.
INEC ta hana shi Takardar Shaidar Lashe Zaɓen ne tun da farko sakamakon iƙirarin da Baturen Tattara Sakamakon Zaɓen Mazaɓar Sanata ta Imo ta Yamma ya yi cewa ya bayyana Okorocha a matsayin wanda ya lashe zaɓen ne bisa tilas.