Hukumomi a babban birnin Mumbai da ke kasar India sun kama wasu Yan Najeriya mutum uku da ake zargi da aikata laifin sata ta yanar gizo.
Rahotanni da jaridar Times of India ta wallafa a yau ya nuna an kama yan Najeriyan mazauna kasar ta India da wasu mutum hudu bisa zargin yin fashi da kwamfuta (Hacking) na kudi a asusun banki sama da guda 2,000.
Wadanda ake zargin sune; Idrish D Costa, Sinedo Christopher, Ifaain Odhu dukkan su yan Najeriya. Sai Irfan A Dehmukh, da Tabiz Deshmukh, da Rajesh Gaikwad, da kuma Nizamuddin Shaikh.
Jaridar ta rawaito cewa wadannan bata gari sun gudanar da mugun aikin su ta hanyar tura sakon waya da zai kai mutum zuwa shafin yanar gizo na bogi wanda ke nuna wa mutum shafin biyan haraji (Income Tax Department).
Daga nan sai mutum ya cike bayanan sa akan shafin na bogi wanda suka hadar da bayanai akan asusun ajiya na banki. Hakan yana basu damar turo sakon manhaja (App) zuwa wayar mutum, wanda da shi ne su ke amfani wajen kwashe kudi daga asusun bankin mutum zuwa nasu.
Mataimakin kwamishinan Yan Sanda Mista J M Yadav ya ce an kama mutanen a ranar Asabar da ta gabata bayan samun korafe- korafe daga al’umma.
Ya kara da cewa, Bata-garin sunyi niyyar sace kudi daga asusun ajiya na mutum 4,727 a fadin kasar India amma zuwa lokacin da aka kama su, sun saci kudin a asusun ajiya na mutum 2,500.
Zuwa yanzu, mutanen suna hannun hukumar Yan Sanda ana gudanar da bincike kafin a mika su zuwa gaban shari’a.