Yau Ake Bikin Ranar Wayar Da Kai Na Duniya Akan Zabiya

168

Mutane da dama a duniya suna fama da larurar zabiya kuma suna fama da tsangwama daga cikin al’umma a fadin duniya. Hakan yasa majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 13 ga watan Juni kowacce shekara domin wayar da kan al’umma.

Wannan rana an ware ta domin al’umma su san cewa mutane masu fama da larurar zabiya suna da hakkin su yi rayuwa kamar kowa, sannan a kare su daga dukkanin nau’ika na tsangwama da wulakanci, da cutarwa, kuma a taimaka musu wajen samun Koshin lafiya.

Larurar Zabiya wata larura ce da ke samun dan Adam na rashin wasu sinadarai cikin kwayar hallita da ake gadon shi, a lokacin haihuwa. Cutar tana iya shafar mata ko maza a kowanni bangare na duniya kuma ba a dauka.

Mutane masu fama da wannan cutar suna fuskantar matsaloli na fata sanadiyyar rashin sinadarin melanin a cikin fatan su, da gashi da Idanu wanda hakan ya ke basu matsala a gani, da fadawa hadarin kamuwa da cutar daji na fata da sauran matsaloli na lafiya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mafi yawanci mutane masu fama da cutar Zabiya suna rasa rayukansu a shekaru 30 zuwa 40 na rayuwarsu saboda rashin samun cikakkiyar kulawa ga lafiyarsu.

Masu wannan larura suna fadawa cikin hadari saboda yadda ake mu’amallantarsu a cikin al’umma. A wasu wurare ana tsokanarsu, ko su fuskanci zagi, ko wariya, ko a daukesu a matsayin wata annoba a cikin al’umma, ko aguje su, ko kuma ayi amfani da sassan jikin su domin yin tsafi.

A shekarar 2010, Majalisar Dinkin Duniyar ta ce an samu rahoton hari tare da kisa guda 700 akan mutane masu larurar a kasashe 28 a nahiyar Afrika, inda tsangwaman yafi kamari.

Hakan yasa ake gudanar da wannan wayar da kai duk shekara domin rage yawan tsagwama gare su tare da samar musu yanci su yi rayuwa kamar kowa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan