Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa, NiMet ta yi hasashen samun yanayin gajimare da ruwan sama tare da tsawa a yawancin sassan ƙasar nan ranar Juma’a.
Rahoton Yanayi da NiMet ta fitar ranar Alhamis a Abuja ya yi hasashen cewa da safiyar ranar Juma’a za a samu tsawa da ruwa a garuruwa kamar Abuja, Lokoja, Makurɗi da Kaduna.
Ta kuma yi hasashen cewa da rana za a samu tsawa tare da ruwan sama a yankin, inda yanayin zafi zai kai digiri 26 zuwa 30, da kuma 17 zuwa 23 a Ma’aunin Celcius.
Hukumar ta ce a safiyar Juma’a, garuruwan Sokoto, Katsina, Gusau da Kano za su samu tsawa tare da yanayin gajimare fiye da sauran jihohin dake yankin.
A cewar NiMet, jihohin Kudancin ƙasar nan kamar Enugu, Owerri, Asaba da Benin za su samu yanayin gajimare a ranar Juma’a da safe.
“Akwai yiwuwar samun tsawa da ruwan sama a yankin da rana da kuma yamma, inda yanayin zafi zai kai digiri 28 zuwa 31, da digiri 21 zuwa 24 a Ma’aunin Celcius.
“Ana kuma hasashen samun yanayin gajimare tare da samun tsawa nan da can da ruwa a yawancin sassan ƙasar nan a cikin awa 24 masu zuwa”, NiMet ta yi hasashen haka.