Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta ce yawan jam’iyyun siyasar da suka shiga zaɓukan 2019 ya haifar mata da matsalolin shirye-shirye da yawa.
Mohammed Haruna, Kwamishinan INEC na Ƙasa mai kula da Jihohin Kwara, Kogi da Nasarawa ya bayyana haka ranar Asabar a Ilori yayin da yake ganawa da manema labarai.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya ruwaito cewa INEC ta shirya taron ƙara wa juna sanin ne don yin bitar yadda ta gudanar da zaɓukan shekara ta 2019.
A cewar Kwamishinan na INEC, akwai ƙararraki 799 da suka taso daga zaɓukan 2019 a ƙasar nan.
Ya ce Jigawa ba ta da ƙara ko ɗaya, Kwara tana da ƙararraki uku, Imo kuma tana da 77.
Mista Haruna ya ce akwai ƙararraki na kafin zaɓe har 800 a faɗin ƙasar nan da suka taso daga zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyu.
“Saboda haka, za ka iya gani, da irin waɗannan matsaloli da muka samu, haƙika akwai buƙatar a dubi yawan jam’iyyun siyasa.
“A gaskiya akwai buƙatar mu yi wani abu game da jam’iyyun siyasa 91, ba kawai yawansu ba wanda a zahirin gaskiya, al’umma tuni sun fara ƙorafi a kai cewa jam’iyyu 93 sun yi yawa”, ya ƙara da haka.
Ya lura da cewa jam’iyyun siyasa 76 ne suka shiga zaɓen Shugaban Ƙasa, yana mai ƙarawa da cewa wannan shi ne babban dalilin da yasa Hukumar ta samu matsala.
“Mun raina irin matsalar shiri wadda ta haifar da girman takardar kaɗa ƙuri’a, takardun rubuta sakamako da sauransu.
“Lokacin da waɗannan kayan aiki za su isa, sai muka gane cewa babbar matsalar shiri ce.
“Mun yi sa’a, muna da Rundunar Sojin Sama ta Ƙasa wadda ta taimaka wajen kai kayan aiki, koyaushe sukan taimake mu”, in ji Mista Haruna.
Kwamishinan ya ce akwai buƙatar a yi bitar Dokar Zaɓe da Kundin Tsarin Mulki don rage yawan jam’iyyun siyasa.
A cewarsa, Kundin Tsarin Mulki da Kundin Tsarin Mulkin sun sauƙaƙa yadda kowa zai iya yi wa jam’iyyar siyasa rijista matuƙar mutumin yana da ofis a Abuja.
Mista Haruna ya ce an shirya taron ƙara wa juna sanin ne don yin bitar zaɓen 2019 don ganin ina aka yi kuskure, a kuma tabbatar da cewa ba a maimaita kura-kuren ba a zaɓuka masu zuwa.
Ya ce bitar za ta taimaki Hukumar ta yi zaɓen da ya fi na bana inganci a jihohin Bayelsa da Kogi nan gaba a cikin shekarar nan.
A jawabinsa, Kwamishinan INEC a Kwara, Malam Garba Attahiru-Madami ya ce maƙasudin taron shi ne a yi bitar yadda aka gudanar da zaɓukan da suka gabata, a kuma kawo hanyoyin da za a magance matsalolin.
Madami, wanda Sakataren Mulki, Martins Borris Chiroma ya wakilta ya shawarci mahalarta taron da su taka rawa ma ma’ana yayin taron.
“Muna so mu ji daga gare ku, yadda zai taimaki INEC ta yi maganin ƙalubalen da ta fuskanta a zaɓukan da suka gabata”, in ji shi.
NAN ya ruwaito cewa Turawan Zaɓe, Mataimaka Turawan Zaɓe masu kula da aikace-aikace daga ƙananan hukumomi 16 na jihar sun halarci taron.
Haka kuma, Turawan Zaɓe, Jami’an Tattara da suka yi aikin zaɓen 2019 a jihar sun halarci taron.