Shahararren masanin Ƙur’anin na Jihar Kano, Malam Gwani Yahuza Gwani Ɗanzarga ya ce bara ba ta da alaƙa da karatun Ƙur’ani.
Malamin ya bayyana haka ne ranar Lahadi a yayin Taron Rufe Daurar Haddar Alƙur’ani Mai Girma da Gidauniyar Qadi Ahmad ke shiryawa a cikin watan Ramadan na kowace a Islamiyya ta Qadi Ahmad dake Rimin Gata, a Ƙaramar Hukumar Ungogo dake Jihar Kano.
Malam Ɗanzarga, wanda shi ne Shugaban Hukumar Kula da Makarantun Ƙur’ani da Islamiyyu ta Jihar Kano, ya ce ko malaman dake koyar da yara karatun Ƙur’ani, ba a ganin ‘ya’yansu suna bara.
Malam Ɗanzarga ya ce kawo yanzu, Hukumar Kula da Makarantun Ƙur’ani da Islamiyyu ta Jihar Kano ta yi wa makarantu kimanin 13000 rijista.
Ya nanata buƙatar da ake da ita ta al’umma da su riƙa yi wa kansu tsare-tsare na ci gaban addinin Musulunci maimakon su jira komai sai gwamnati ta yi.
A jawabinsa, Babban Jami’in Shirya Daurar, Malam Aliyu Ibrahim Sani Mainagge ya ce a bana an gabatar da Daurar ne da ɗalibai 93, maza 57, mata 36.
A cewarsa, wannan shi ne adadi mafi yawa da aka taɓa samu tunda aka fara gabatar da Daurar, shekaru tara da suka gabata.
“Haka kuma, a wannan shekarar, an sami dattijo ɗan shekaru 53 da ya zo ya tare a wannan makaranta, yana kwana yana karatun Alkur’ani a ƙoƙarinsa na haddace Alƙur’ani.
“Haka kuma, an sami dattijuwa ‘yar shekaru 50, ita ma tana ƙoƙarin ganin ta haddace Alƙur’ani Mai Girma”, in ji Malam Mainagge.
Ya ƙara da cewa a ƙarshen Daurar, an samu ɗalibai 10 da suka kammala izifi 60, sai ɗalibai 15 da suka kammala daga izifi 30 zuwa 40 zuwa, sai ɗalibai 25 da suka kammala daga izifi 15 zuwa 20, sai ɗalibai 15 da suka yi daga izifi 10 zuwa 15, sai kuma sauran ɗalibai da suka yi daga izifi 10 zuwa ƙasa.
Malam Mainagge ya ce daga cikin matsalolin da Daurar take fuskanta akwai ƙarancin ɗalibai dake halarta, ƙarancin kuɗi da kuma kasa aiwatar da shirin yadda ake so.
A jawabinsa, Shugaban Kwalejin Nazarin Addinin Musulunci da Shari’a ta Aminu Kano, Farfesa Balarabe Abubakar Jakada wanda Magatakardar Makarantar ya wakilta, ya taya ɗaliban da suka halarci Daurar murna, ya kuma yi alƙawarin cewa duk ɗalibin da yake da sha’awar nazarin Kimiyyar Ƙur’ani, idan ya je Kwalejin da Takardar Shaidar Halartar Daurar za su ɗauke shi kai tsaye, kuma zai yi karatu kyauta.
Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai shahararren malamin Ƙur’ani, Gwani Yahuza Gwani Ɗanzarga, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, tsohon Shugaban Kwalejin Nazarin Addinin Musulunci da Shari’a ta Aminu Kano, Dakta Nurudeen Musa, Magatakardar Kwalejin Nazarin Addinin Musulunci da Shari’a ta Aminu Kano, Limamin Galadanci, Malam Faruƙ Sani Galadanci da Dagacin Rimin Gata Abuddarda’i Yahya.
A ƙarshen taron an ba da kyaututtuka ga ɗalibai, malamai da wasu mutane da suke bada gudunmawa wajen ci gaban addinin Musulunci.