Ganduje zai kafa Ma’aikatar Harkokin Addini

43

Gwamnatin Jihar Kano za ta kafa Ma’aikatar Harkokin Addini domin yin maganin matsalolin dake fuskantar harkokin addinin Musulunci da dokokinsa.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ranar Lahadi a Kano yayinda yake yi wa wasu malamai jawabi a wani taron addu’o’i da aka shirya domin samun zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a jihar.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa tana ba addini muhimmanci sosai saboda rawar da yake takawa wajen inganta halayya da tarbiyya.

“Ma’aikatar, idan aka kafa ta, za ta zama wata gada tsakanin mabiya addinai daban-daban a jihar nan.

“Batutuwan aure za su kasance wani ɓangare na aikace-aikacenta, ma’aurata da suka rabu sun kasance wata matsala da gwamnatinmu ta damu da ita sosai. Za mu ba Ma’aikatar dama da tunkari wannan al’amari”, in ji Gwamna Ganduje.

Sauran abubuwan da Ma’aikatar za ta mayar da hankali, a cewar Gwamnan sun haɗa da rarraba Zakka da kula da hukumomin Musulunci kamar Hukumar Zakka, Hukumomin Hubusi, Shari’a da sauransu.

Gwamnan Ganduje ya ƙara da cewa Ma’aikatar za kuma ta yi maganin barace-barace a tituna, za kuma ta fito da hanyoyin kula da ƙananan yara kamar yadda tsare-tsaren Musulunci suka tanada, musamman ilimi da kuma ci gaba da neman ilimi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya ruwaito cewa malamai 300 ne suka halarci taron addu’o’in, da ya haɗa da malamai maza 200, malamai mata 100.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan