Hukumar Hana Cin Hanci Ta Binciki Yadda Gwaggon Biri Ya Hadiye Kusan Naira Miliya Bakwai A Gidan Zoo – Inji Gwamnan Kano

157


Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin gudanar da bincike akan batun batan kudi har naira miliyan shida da dubu dari takwas a gidan Zoo na jihar.

Gwamnan ya yi kira ga hukumar hana ci hanci da rashawa ta jihar (Kano State Anti Corruption Commission) da ta yi bincike kan aukuwar lamarin.

Gwamnan ya bada umarnin ta cikin sanarwa da ya fitar ta hannun babban sakataran yada labaran gwamnati, Abba Anwar a jiya lahadi, 16 ga watan Yuni shekarar 2019.

Mal. Abba Anwar ya ce gwamnan ya bada umarnin gudanar da bincike ga hukumar a ranar Jumu’ar da ta gabata domin gano gaskiyar lamari, inda ma’aikatan gidan zoo na jihar suka ce wani gwaggon biri ya hadiya kudi da akalla ya kai naira miliyan bakwai da gidan ya tara, ta hanyar karban kudin shiga daga masu zuwa kallo musamman a lokacin bikin sallah.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan